Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti{a.s} - ABNA - nakalto wani dan yankin wanda ya fada masa cewa ‘yan tawayen sun sake komawa garin Lalibela da karfinsu a jiya Lahadi. Kafin haka dai sojojin gwamnatin kasar karkashin jagorancin firai ministan kasar sun tilastawa ‘yan tawayen yin nesa daga birnin AdiaAbba babban birnin kasar sannan sun sami nasarori da dama kan su a lardin Amhara da wasu wurare.
Tun shekarar da ta gabata ce sojojin gwamnatin Abiy Ahmed suka fara yakar ‘yan tawayen na Tirgay. Labarin ya kammala da cewa a halin yanzu dai ana fafatawa tsakanin sojojin gwamnati da ‘yan tawayen a wurare da dama.
342/